
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya mayar da martani ga kalaman Sanata Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, wanda ya yi suka kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na cigaba da barin Mataimakinsa, Kashim Shettima akan karagarsa.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasar, Stanley Nkwocha, ofishin ya bayyana kalaman na Baba-Ahmed a matsayin” kalamai marasa kan gado” waɗanda Tinubu da mataimaki nasa ba su da lokacin sauraronsu, kasancewar sun mayar da hankali kan ayyukansu na gina ƙasa.
Sanarwar ta kuma bayyana irin nasarorin da Shettima ya samu da ma ƙwarewarsa akan ayyukan da suka haɗa da gogewarsa a harkar koyarwa da bayar da ilimi da kasancewarsa ma’aikacin banki, kwamishina, sannan gwamna kana sanata, kafin ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Shettima na biyayya ga shugaba Tinubu kamar yadda yake nuna jajircewarsa kan tabbatar da ajandar sabunta fata ta ‘Renewed Hope Agenda’.
Ofishin ya kuma tunatar da Baba-Ahmed abubuwan da suka faru a baya, da suka haɗa da cire shi daga Majalisar Dattawa a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da maguɗin zaɓe inda ta ƙara da cewa, zantukan na Baba Ahmed watakila ba za su rasa nasaba da ƙwaɗayinsa na ɗarewa kowace irin kujerar mulki ko da kuwa ta haramtacciyar hanya ce, musamman ma kujerar Mataimakin Shugaban ƙasar, wadda ya sha kaye a takararta a zaɓen 2023 sakamakon karawarsa da gogaggen ɗan siyasa ɗan asalin Arewa wanda ke da tarin abin faɗa na nasarori a ajandar sabunta fata ta Shugaban Kasa.
