Daga WAKILINMU a Sakkwato
Mashawarci na musamman ga Ministan Ilimi kan harkokin almajirai da yaran da basa zuwa makaranta, Dakta Balarabe Shehu kakale (Barden Tsangayu da Makarantun Allo na ƙasar Hausa), ya shawarci ýan Nijeriya da su yi gaggawar shiga shirin nan na “Me Ka Iya Ba Me Ka Karanta Ba, wato TVET” wanda Gwamnatin Tarayya ta fito da shi.
Hon. Balarabe Shehu ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da wata muƙala a wajen taron wayar da kan al’umma na wuni guda akan muhimmancin shirin, wanda cibiyar yaɗa addinin Musulunci ta IET dake Jihar Sakkwato ta shirya wa ƙungiyoyin addinin Musulunci da ke jihar, inda ya ce yanzu haka dubban mutane sun cike shirin ta manhajar da aka sanar tun a kwanakin baya.
Hon. Kakale wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne ya ƙara da cewa akwai buƙatar masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi da harkokin da’awa musamman ƙungiyoyi, su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma akan sabon shirin, wanda ma’aikatar ilimi ta samar, bisa la’akari da ɗumbin alfanun da za a samu har ma da sauyin da zai kawo a sha’anin ilimi ga ƙasa baki ɗaya da haɓɓaka tattalin arziƙi.
A cewar sa, “An fito da shirin ne don sake farfaɗo da darajar ilimi ta hanyar inganta tsarin ta yadda zai dace da zamani da kuma fuskantar ƙalubalen da ke cikin manhajar Ilimi ta ƙasa, domin amfanar da al’umma da kuma koya musu sana’o’in da aka gada a wajen iyaye da kakanni, maimakon karatu kaɗai.”
A nasa jawabin shugaban cibiyar yaɗa addinin Musulunci ta Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sokoto), ya ce maƙasudin shirya taron shi ne don gayyato Honarabul Kakale, domin ya zo ya yi wa al’umma bayani kan yadda sabon shirin zai bada gudunmawa don kar a bar jihar a baya.
A cewar malamin, “Muna goyon bayan duk wani abu da zai kawo cigaban ilimi da addinin Musulunci, don haka muna kira ga dukkan mahalarta taron da su tashi tsaye wajen ganin sun bada tasu gudunmawar ta hanyar samar da tsarin yi wa al’ummar jihar rijista kyauta daga IET saboda a ƙarfafa musu gwiwa akan shirin.
Taron ya samu halartar ɗumbin al’umma da sauran masu ruwa da tsakin da ke sassan jihar.
