Gwamnatin Kano da haɗin gwiwar PLANE ta shirya bita kan samar da hanyar inganta harkokin ilimi

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar ƙungiyar nan mai tallafawa harkar ilimi a Nijeriya wato PLANE, ta shirya bita kan bijiro da tsare-tsaren da za su inganta ɓangaren ilimi a jihar Kano na matsakaicin zango daga shekaara ta 2026-2028.

Bitar za ta yi duba na musamman kan kyawawan manufofin da ake son cimma a ɓangaren ilmi, kawo mafita ga matsalolin ilmi a Jihar Kano tare da bayar da fifiko ga hanyoyin da za a taimakawa ɓangaren ilmi.

Taron wanda ake gabatar da shi a jihar Kaduna ya ƙunshi mahalarta daga ma’aikatar ilmi, da Ma’aikatar Kuɗi da Ma’aikatar Kasafi da tsare-tsare da sauran masu ruwa da tsaki kan harkar ilmi.

Bitar ta fara ne da gabatar da jawabi na maigirma Kwamishinan Ma’aikatar ilmi ta Jihar Kano Gwani Dr. Ali Haruna Makoda wanda babban Sakatare Alhaji Bashir Baffa Muhammed ya wakilta.

An gabatar da maƙaloli daban-daban da suka haɗa da manufar tsare-tsaren da za su inganta harkar ilmi a matsakaicin zango da rawar da ake buƙata mahalarta bitar su taka wajen tabbatar da shirin gami da yin waiwaye kan manufofin ilmi da sakamakon da ake so a cimma.

Wannan bita na yin nuni ga ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kano na bunƙasa ɓangaren ilmi wanda ya zo daidai da kyawawan ayyukan da gwamnatin take aiwatarwa.

By ukarofi