An ƙaddamar da gasar kacici-kacicin kimiyya da fasaha na Abba Gida-Gida

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanar da gasar kacici-kacici na ‘yan makarantun kimiyya da fasaha na jihar Kano na Abba gida gida da aka ƙaddamar a ɗakin taro na Gidan Gwamnati a ranar Asabar.

Babban sakataren Hukumar makarantun kimiyya da fasaha na jihar Kano Farfesa ɗahiru Saleh Muhammad ya ce zuwan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf  ya ƙaddamar da wata doka akan farfaɗo da ilimi.

Ya ƙara da cewa dokar ta farfaɗo da ilimin kimiyya da fasaha da akayi a jami’ar Bayero ita ta basu damar duba mene ne ake yi a ilimin kimiyya da fasaha a baya da yanzu ba ayi sai suka gano ba a yin wasu abubuwan har ma da kacici-kacici irin wannan shine suka dawo da shirya gasar kacici-kacicin na kimiyya harma suka ƙara da na nuna fasaha na makarantun fasaha.

Ya ce hukumar makarantun kimiyya babu abinda za su cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda yana bada kulawa gare su wanda shi ya sa suke bijiro da abubuwan inganta ilimin kimiyya da fasaha ake ta samun nasara akai.

Farfesa ɗahiru Saleh Muhammad Babban sakataren Hukumar makarantun kimiyya da fasaha na Kano ya ce makarantun hukumar 49 ne suka shiga cikin gasar sun kuma rarraba su ne shirya shida an soma buɗewa  da shirya ɗaya ragowar kuma zasu yi gaba ɗaya, a  kuma za aje  zagaye na biyu har zuwa ƙarshen gasar.

A yayin buɗe taron gasar kacici kacicin mai baiwa Gwamna Shawara akan Kimiyya da fasaha Hon. Habibu El-yakub ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kano take na ganin ta kyautata harkar ilimi ta warewa ilimi kaso mafi tsoka a kasafin kuɗi da kuma tura ɗalibai ƙasashen waje ƙaro ilimi da samar da kayan aiki a makarantun firamare a dana Sakandire dake  faɗin jihar Kano.

Daga cikin mahalarta taron na ƙaddamar da buɗe gasar kacici kacicin  Abba Gida gida na makarantun kimiyya da fasaha na jihar Kano akwai babban sakatare a ma’aikatar ilimi na jihar Kano, Alhaji Bashir Baffa wanda ya wakilci Kwamishinan ilimi na jihar Kano Gwani Ali Bukar Makoɗa.

By ukarofi