Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Yanzu dai zaman lafiya ya fara dawowa a ƙaramar hukumar Ɗanmusa wannan kuwa ya biyo bayan zaman sasanci da aka yi tsakanin al’ummar yankin da ‘yan ta’adda.
Wani mazaunin garin Ɗanmusa da bai yadda a faɗi sunan sa ba ya bayyana cewa rabon su da bin hanyar garin Ɗanmusa zuwa ‘Yantumaki da wasu ƙauyuka ya kai shekara biyar “sai Yanzu da zaman lafiya ya dawo,”a cewar sa.
Ya ce a yanzu dai harkokin kasuwanci da zirga zirga na ababen hawa ya dawo a tsakanin garuruwan da ke yankin.
Haka kuma bayan zaman sulhun suma ‘yan bindigan sun fara cuɗanya da mutanen gari da cigaba da gudanar da kiwon dabbobin su.
Mazaunin garin na Ɗanmusa yayi kira ga al’ummar yankin da tubabbun ƴan bindigan da suyi haƙuri da juna”abinda akayi ya wuce a yafewa juna,”yace.
Ɗaya daga cikin tubabbun yan bindigan da a kayi magana da shi ta wayar salula yayi kira ga shugabanni da su riƙa adalci wajen kama waɗanda ake zargi da aikata ta’addanci domin a cewarsa yawancin waɗanda ake kamawa zaka ga basu ji ba basu gani ba.
Haka ma noma da kiwo ya dawo a ƙauyukan ‘Yantumaki yankin da shima yayi ta fama da rashin tsaro sakamakon hare haren ƴan bindiga.
Yanzu dai zaman lafiya ya dawo a ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Safana da Ɗanmusa.
Fatan suma sauran ƙananan hukumomin da suka rage masu fama da rashin tsaro zasu yi zaman sulhu domin cigaban yankin su.
Ita dai gwamnatin Jihar Katsina ta nanata cewa ba zata yi sulhu da ƴan ta’adda ba sai da in su ne suka buƙaci a yi.
