‘Yan bindinga sun yi awon gaba da basarake a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari cikin dare a garin karaɗuwa da ke ƙaramar hukumar Matazu, Jihar Katsina, inda suka sace hakimin garin, Alhaji Abdullahi Bello.

Rahotanni sun bayyana cewa a yau Asabar, 5 ga Yuli, wasu mahara da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun kai farmaki, bayan razanar da mazauna garin da harbe harben bindinga sai suka wuce gidan hakimin garin, suka kuma tisa ƙeyarsa zuwa cikin daji.

Bakatsine wani mai kawo rahotanni kan tsaro da ta’addanci ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X, da safiyar yau Asabar 5 ga watan Yulin 2025.

“A daren jiya, ’yan bindiga sun sace hakimin Karaɗuwa (Magajin Garin Karaɗuwa), Alhaji Abdullahi Bello Karaɗuwa.

“Karaɗuwa gari ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar matazu a Jihar Katsina.” In ji shi.

Har zuwa haɗa wannan rahoto rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina bata yi ƙarin bayani ba game da lamarin.

By ukarofi