Ba mu yarda da karɓe iko daga haɗaka ƙarƙashin David Mark ba – Shugabannin ADC na jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rikici na neman ɓarkewa a jam’iyyar adawa ta ADC a yayin da shugabanninta na jihohi da dama suka nuna rashin amincewarsu game da sabunta tsarinta da sabuwar haɗaka ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar ta yi.

Jam’iyyar, wadda aka ƙarfafa da nufin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ta fara fuskantar tsaiko daga jagorori a mataki na ƙasa.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da tsohon Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Ralph Nwosu ya yi na rushe tsare-tsaren jam’iyyar da nufin kafa ta ƙarƙashin ikon ƴan siyasar haɗaka da suka shiga cikinta a kwanan nan.

Lamarin da ya sa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark ya zama shugaba na riƙo ƙwarya, tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola a matsayin sakatare, sai kuma tsohon ministan wasanni Bolaji Abdullahi a muƙamin sakataren yaɗa labarai.

Akan haka ne da dama daga cikin jagororin jam’iyyar a mataki na jihohi suka ƙalubalanci sabunta tsare-tsaren.

Shugaban ADC a Benuwai, Elias Adikwu ya bayyana hakan a matsayin karan-tsaye ga darajoji da ikon jam’iyyar da dimukraɗiyya ta ba ta, yana mai cewa lallai ba sa tare da su kuma ba za su amince ba.

A wata hira da manena labarai, Adikwu ya ƙalubalanci halacin kafa tawagar jagorancin riƙo, inda ya ce dokokin jam’iyyar ba su bada damar haka ba.

By Babaji