
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya rage farashin litar fetur, inda ya ke sayerwa a Birnin Tarayya Abuja, Kaduna da Kano akan N910.
Hakan na nufin an samu ragin Naira 35, wato ƙasa da N945 da ake sayerwa a baya.
An ga yadda wasu gidajen mai suke sayerwa akan N935 a yankunan Lugbe da Airport Road dake birnin tarayyar.
Lamarin da ya samu a sakamakon sauka da farashinsa ya yi a kasuwannin duniya, inda ganga guda na ɗanyen mai ya koma Dala 68.30 a ranar 4 ga watan Yuni.
Akan haka ne Matatar Ɗangote ta rage farashin sayerwa ga masu dako zuwa N840 a ranar 1 ga watan Yuli.
A ranar 23 da 24 ga Yuli ne za a yi zama da ƴan kasuwa a ƙarƙashin jagorancin Hukumar kula da harkokin Ɗanyen mai ta Ƙasa (NMDPRA) akan matsalolin raba mai a fannin da samar da tsare-tsaren farashi, kamar yadda Francis Ogaree na hukumar ya bayyana.
