Elon Musk ya kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka

Spread the love

A wani sabon babi da zai iya sauya tsarin siyasar Amurka, attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya bayyana ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa da aka raɗa wa suna “American Party” domin ƙalubalantar manyan jam’iyyu biyu na sananu, wato Republican da Democrat.

Musk, wanda ya taɓa zama babban mai goyon bayan Shugaban ƙasa Donald Trump, ya bayyana wannan matakin a ranar Lahadi, kwana guda bayan gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayi ta yanar gizo a shafin ɗ wadda aka sani da Twitter a can baya. A cikin wannan ƙuri’a, kashi 65% na masu kaɗa ƙuri’a sun nuna goyon bayan ƙirƙirar sabuwar jam’iyya.

“Kashi biyu cikin uku sun nuna buƙatar sabuwar jam’iyya. Kuma za ki same ta,” inji Musk a ɗ

Ya ƙara da cewa, “Tsarin siyasar Amurka ya koma na jam’iyya ɗaya.”

Elon Musk ya bayyana cewa, tsarin siyasar Amurka ya dusashe, inda ya zargi jam’iyyun biyu da yin haɗin baki wajen “lalata tattalin arzikin ƙasa ta hanyar almubazzaranci da cin hanci.”

Ya ce: “A yau an kafa American Party domin dawo muku da ‘yancin ku na gaske.”

A kwanakin baya, Musk ya daɗe yana wallafa ra’ayoyinsa a ɗ game da buƙatar kafa sabuwar jam’iyyar da za ta yiwa tsarin da ya kira “na uniparty” barazana. A cikin wani rubutu da ta yi a ranar 4 ga Yuli, ranar ‘Yancin Kai a Amurka, ya tambayi mabiyansa:

“Shin lokaci ya yi da za mu samu ‘yanci daga tsarin jam’iyya biyu? Ya ya kuke gani, a kafa America Party?”

Musk ya ce, jam’iyyun biyu sun faɗi a kan burin yawancin ‘yan ƙasa, yana nuni da cewa, kashi 80 cikin 100 na Amurkawa na cikin matsakaicin ra’ayi, ba su goyon bayan matsanancin ra’ayi daga hagu ko dama ba.

“Wannan ƙungiyar sabuwar jam’iyya ce don masu hankali da tunani tsaka-tsaki,” inji shi.

A cewar masana, wannan mataki na Elon Musk bai rasa nasaba da wata ɓaraka da ta kunno kai tsakaninsa da Donald Trump dangane da wata babbar dokar kasafin kuɗi da aka fi sani da “One Big Beautiful Bill.”

Wannan doka da Trump ya daɗe yana ƙoƙarin tabbatarwa, ta ƙunshi muhimman manufofinsa da za su ba shi damar aiwatar da ajandarsa ba tare da dogon tsarin amincewa daga majalisa ba.

Musk, a gefe guda, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan dokar, inda a ranar Juma’a ya goyi bayan suka daga Sanata Rand Paul wanda ya ce dokar za ta haifar da gagarumin giɓi a kasafin kuɗi.

Musk ya sake ɗora wannan suka a ɗ tare da amfani da alamar “💯” don nuna goyon bayansa ɗari bisa ɗari.

Masana siyasa na ganin wannan mataki na iya girgiza tsarin siyasar Amurka, musamman duba da shahararsa da kuɗi da tasiri da Musk ke da su. A cewar wani masanin siyasa a jami’ar Columbia: “Idan har Elon Musk ya ɗauki siyasa da gaske kamar yadda ya ɗauki fasaha da kasuwanci, to jam’iyyun gargajiya za su fuskanci matsin lamba na gaske.”

Yanzu dai hankula sun karkata wajen ganin ko “American Party” za ta samu tagomashi daga masu kaɗa ƙuri’a a zaɓe mai zuwa, ko kuwa za ta kasance ɗaya daga cikin jam’iyyun da ke da ƙima a kalmomi amma ba a zaɓe.

Zuwa yanzu, Musk bai bayyana ko shi da kansa zai tsaya takara a 2028 ba, amma tsarin tafiyar sa na nuna cewar yana da niyyar janyo hankalin masu kishin sauyi daga ƙungiyoyin da suka saba da siyasar Amurka.

By ukarofi