Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kundin dokokin tsaftar muhalli da ta fassara zuwa Hausa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta ƙaddamar da kundin dokokin tsaftar muhalli da ta fassara da harshen Hausa.

Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.

Ya ce an fassara kundin dokoki da kuma kundin ƙa’idojin kula da gurɓatar muhalli ne domin “sauƙaƙa fahimta da kuma cigaba da wayar da kan jama’a akan dokokinmu na tsaftar muhalli”

Hashim ya bayyana cewa tun a watan Afrilu ya ɗauki alƙawari cewa za a fassara su zuwa harshen Hausa. 

“Yau, cikin yardar Allah, ina sanar da ku cewa mun kammala wannan aikin tare da samar da cikakkun kundin da kowa zai iya saukewa kai tsaye tare da na turancin su,” inji Kwamishinan..

Kundin sun haɗa da – Kundin Dokar Kula da Gurɓatar Muhalli ta Jihar Kano, 2022 (Kano State Enɓironmental Pollution Control Law 2022).

Da kuma ƙa’idojin Kula da Gurɓatar Muhalli da Shawo kan Shara ta Jihar Kano, 2025 (Kano State Enɓironmental Pollution and Waste Control Regulations 2025).

Ya kuma ce za a iya samun waɗannan ƙunshi ta yanar gizo akan adireshin  https://environment.kn.gov.ng/resources

“Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da su karanta su kuma bi waɗannan dokoki da ƙa’idoji domin rashin sani ba zai zama hujja ba,” inji shi.

By ukarofi