Masoyin Buhari ya bai wa mahaƙan kabarin tsohon shugaban ƙasa kyautar Naira miliyan ɗaya 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani masoyin marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Alhaji Sirajo Yazid-Abukur, ya yi alƙawarin bayar da Naira miliyan ɗaya ga ma’aikatan da suka haƙa kabarin da aka binne marigayin a gidansa da ke Daura.

Yazid-Abukur, wanda shi ne Manajan Darakta na Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Jihar Katsina (KASSROMA), ya bayyana hakan ne a Katsina a ranar Alhamis, biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta na waɗannan ma’aikata.

A cewarsa, shugaban tawagar masu haƙon kabarin, Malam Muhammad Ali, zai karɓi Naira 500,000, yayin da sauran mutane biyu za su karɓi Naira 250,000 kowannensu.

Ya kuma bayyana cewa ya ba su kyautar kuɗin ne don su yi jari da shi.

By ukarofi