Buhari: Ƙasar China ta yi rashin babban aboki – Xi Jinping

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasar China, ɗi Jinping, ya miƙa saƙon ta’ziyyarsa ga Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, bisa rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa ranar Laraba a madadin gwamnati da al’ummar China, ɗi ya ce suna taya gwamnatin Nijeriya da iyalan tsohon shugaban alhinin rasuwarsa.

Ya bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban ƙasa da haɗin kanta, kuma ana girmama shi a faɗin duniya.

Shugaban na China ya ce zamanin mulkin Buhari, ya kyautata ƙawance da kasarsa da ma alaƙarta da sauran ƙasashen Afirka, inda ya ce rashinsa ya sa ƙasarsa ta yi rashin babban aboki.

ɗi Jinping ya kuma ce China na mutunta alaƙarta da Nijeriya kuma a shirye take ta ci gaba da ganin kyakkyawar alaƙar ta ci gaba da wanzuwa.

By ukarofi