Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Kwamishina yaɗa labarai na jihar Abia, John Kalu, ya ba da labarin yadda ya haɗu da Buhari inda bambance tsakanin ya shugaban Nijeriya na lokacin da ake zargin na bogi ne – Jubril al-Sudani.
Kalu wanda ya riƙe muƙamin kwamishina daga shekarar 2015 zuwa 2023, a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu, ya yi bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook cikin wani dogon rubutu da ya yi a ranar Talata.
Buhari ya riƙe shugabancin Nijeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan bayan fama da jinya a ranar Lahadi yana da shekaru 82.
Tsohon shugaban dai an binne shi ne a gidansa da ke Daura a jihar Katsina a ranar Talata.
A shekarar 2018 a lokacin mulkin Buhari na farko, an yi ta samun ka-ce-na-ce game da mutuwarsa a 2017 da zargin an maye gurbinsa ne da wani daban mai kama da shi da ake kira Jubril daga ƙasar Sudan da ke yankin Afirka maso gabas.
Buhari ya taɓa shafe watanni a ƙasar Landan sakamakon wata rashin lafiya da yake fama da ita a can.
Jagoran ƙungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, da ke rashin kafa ƙasa mai zaman kanta a yankin Kudu maso gabashin Najeriya na daga cikin mutanen da suka yi ta yayata zargin.
Kanu wanda a yanzu yake fuskantar zarge-zarge na cin amanar ƙasa, gwamnatin Buhari ta fara kama shi a lokacin, ya ce, makusanta Buhari sun yi alƙawarin ƙin bayyana cewa Buhari da ake gani ba na gaskiya.
Sai dai a cikin rubutun da ya yi a shafina na Facebook, Kalu ya ba da labarin yadda ya haɗu da Buhari ne a shekarar 2018 wanda ya tabbatar da cewa wannan Buharin na gaske ne.
“A baya a shekarar 2018, Ina cikin wakilan da aka aika su sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MOU) ga ƙungiyar tattalin arziƙi da gwamnatin tarayya wacce ta yi alƙawarin zuba hannun jari Naira biliyan 20 wajen ayyukan raya ƙasa a gwamanti Buhari.”
“Wannan ce dama ta ta biyu ta haɗuwa da shugaban ƙasa Muhammed Buhari kuma ga-ni-ga-shi duk da a baya na sha haɗuwa da shi a lokacin ziyararsa zuwa Aba a watan Janairun 2015 domin yaƙin neman zaɓe a titin Etche Road APC,” ya bayyana.
Tsohon kwamishinan ya ce, bai taɓa yarda da wannan shaci-faɗin ba ko ƙoƙarin tabbatarwa har kawo lokacin da ya haɗu da Buhari a 2018 a fadar shugaban ƙasa.
“A gaskiya a lokacin da muka je fadar shugaban ƙasa, Aso Rock, abin da ke zuciyata shi ne na tabbatar da abin da gaskiyar idan Buhari ne shi ne wanda muka taya murna kifar da gwamnatin Shagari a 1983 da kawo shirin yaƙi da rashin ɗa’a for ousting the ‘corrupt’ (WAI) tare da mataimakinsa Tunde Idiagbon ko kuwa ‘Jubril al-Sudani’ ne kamar yadda wasu maƙiyansa ke ƙokarin tilasta wa mutane su yarda da iƙirarinsu.”
“A baya na san cewa Buhari shi ne dan kyakkyawan janar ɗin na 1983 wanda ke da wa bakar alama a goshinsa da ake gaya mana ya same shi ne saboda yawan sa goshinsa a ƙasa kamar yadda Musulmai suke yi. Sannan na san yana da tsayi da doguwar haɓa da murmushi da kuma yadda yake tafiya,” ya bayyana.
Sannan ya cigaba da cewa: “A matsayina na masanin kimiyya na yi amanna da hanyar lura da gwaji, don haka na ce zan gwada wannan gaskiyar.
“Buharin da na gani a ranar shi ne dai Buharin da na gani a Aba a shekarar 2015, kuma na lura shi mutum ne mai gaskiya da barkwanci.
“A lokacin da muka tafi ɗaukar hoto gabaɗaya bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, kuma a lokacin da suke gaisawa da gwamna Okezie Ikpeazu, na matsa kusa sabods ina so na tabbatar da wani abu.
“A lokacin da gwamna Ikpeazu ya gabatar da wani sanan nan lauya, sai shi lauyan ya tuna wa Buhari cewa sun taɓa aiki tare a shekarar 2003 har kawo 2015. Sai Buhari cikin barkwanci ya ce masa, ‘ kana tare da ni a 2003 da 2007 da 2011 a lokacin da nake ta faɗuwa zaɓe amma ba ka bar ni ba sai a 2015 a lokacin da na ci zaɓe?’ Ka sa daina murmushi na yi, duk da lauyan na san har ya bar fadar shugaban ƙasa bai ji daɗi ba.”
