
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Juma’a ne Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Kano da nufin jajenta wa iyalai, gwamnati da ɗaukacin al’umma bisa rasuwar Hamshaƙin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata.
Shugaba Tinubu ya bayyana mamacin a matsayin mai nagarta da tausayin al’umma wajen inganta rayukansu, yana mai cewa rayuwarsa abin kwaikwayo ne a gare su.
An yi wa Ɗantata, wanda ya shafe shekaru 94 a Duniya jana’iza ne a Madinah, Saudiyya a ranar 1 ga watan Yuli bayan rasuwarsa a Birnin Dubai.
Saidai, ana cecekucen siyasa akan ziyarar shugaban ƙasar duba da yadda ya yi gum akan rikicin masarautar Kano da ƙaurace wa ziyartar gidan gwamnati ko fadar sarki, wanda zuwa wuraren na daga cikin tsarin ziyarar shugaban ƙasa ga jiha.
Lamarin da ya haifar cecekuce a tsakanin masu sharhi kan harkokin siyasa da ɗaukacin al’umma, duk da cewa wasu na ganin hakan wani mataki ne na ƙaurace wa cigaba da ruruta wutar rikicin Masarautar Kano.
Duk da cewa an kimtsa wa zuwan Shugaban ƙasar a fadar ta Gidan Rumfa wajen shirya dawakai da yin wasu gyare-gyare, an bar Sarki Sanusi cikin jiran tsammani. Haka ma a Gidan Gwamnatin jihar, inda aka tsayar da zirga-zirga saboda tsammanin zuwan nasa.
