A karon farko, Dino Melaye ya bayyana a matsayin lauya a kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Malaye ya shiga kotu a matsayin lauya, sakamakon koma wa harkar shari’a, shekaru da dama ana damawa da shi a harkar siyasa.

Dino, wanda ya yi shiga irin ta lauyoyi, an gan shi ne a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, a yayin wani zama ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Emeka Nwite.

Tsohon ɗan majalisar dokokin yana ɗaya daga cikin ɗalibai sama da guda 5,000 da aka yaye a matsayin lauyoyin a farkon watan Yuli, biyo bayan kammala digirinsa a fannin daga Jami’ar Baza dake Abuja.

Jigon jam’iyyar adawa ta PDP ya wakilci mazaɓar Kogi ta Yamma ne a majalisa ta takwas.

By Babaji