Ba ni da tabbacin tsaro a gare ka kan ziyarar da babu sanarwa – Gwamnan Edo ga Peter Obi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya gargaɗi tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takara shugaban ƙasa a Jam’iyyar LP, Peter Obi, game da tsaron lafiyarsa matuƙar ya ziyarci jihar ba tare da sanar da gwamnati ba gabannin haka.

A lokacin da ya ke magana Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas yayin karɓar Hon. Marcus Onobun zuwa jam’iyyar APC, Gwamna Okpebholo ya ce ba zai amince da wata ziyara daga ƴan adawa ba tare da sanarwa ba.

Ya ce, duk abinda ya faru a yayin irin ziyarar, to kada a zargi kowa akan abin fashewa ka iya faru a sakamakon haka, saidai wanda ya yi ziyarar ya zargi kansa.

Gwamnan ya faɗi haka akan ziyarar da Peter Obi ya kai a jihar kwanan nan, inda ya bada tallafin Naira miliyan 15 ga wani asibiti a Benin, Babban Birnin jihar.

Ya kuma alaƙanta ziyarar ta Obi da ɓarkewar rikici tsakanin ƴan ƙungiyoyin asiri a wasu sassan jihar.

Lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan mutane guda 12, wandavkawo yanzu hukumomi na cigaba da ƙoƙarin dakatarwa.

By Babaji