PDP ta ayyana ranar babban taronta na ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar PDP ta kammala zaman kwamitin zartarwata (NEC) inda ta ayyana ranakun gudanar da babban taronta a watan Nuwamba, 2025.

A yayin zaman, wanda aka yi a Abuja ranar Alhamis, aka ayyana ranakun 15 da 16 ga Nuwamba a matsayin lokacin babban taron wanda za yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.

Kwamitin Zartarwar jam’iyyar ya tabbatar wa mambobi da ɗaukacin ƴan Nijeriya cewa PDP tana nan da ƙarfinta kuma kan ƴaƴanta a haɗe ya ke wajen ganin ta cimma nasarorin da ta saka a gaba.

Ya umarci Shugaban jam’iyyar, Ilya Damagum da Sakatarenta, Sanata Samuel Anyanwu da su rubuta wa Hukumar Zaɓe (INEC) batutuwan da suka shafi lokaci, wuri da ababen da za a tattauna a babban taron kamar yadda dokar zaɓe ta hukunta.

Haka kuma kwamitin ya amince da mambobin kwamitocin taron da na shiyyoyi domin tabbatar da gaskiya da adalci a yayin gudanar da harkokin taron.

Daga ƙarshe, kwamitin ya ɗage zaman da ya saba yi zuwa ranar 25 ga watan Agusta, 2025.

By Babaji