Shugabancin RTEAN: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da sahihancin zaɓen Musa Mai-Takobi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zamanta a Abuja ta tabbatar da Dakta Musa Muhammed Mai-Takobi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri da Saukar Ma’aikatan Sufuri, wato RTEAN, lamarin da ya kawo ƙarshen ta taƙaddamar shugabancin ƙungiyar.

Alƙalan Kotun da suka haɗa da Mai Shari’a Abba Bello Muhammed da Mai Shari’a Eberechi Suzette Nyesom-Wike ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamma Akawu Barka sune suka tabbatar da hukuncin bayan sun yi fatali da karar da Mr. Eriyo Osakpamwan, ya shigar a gabanta tun a shekara ta 2021 kan ƙalubalantar shugabancin Musa Muhammed Maitakobi, inda suka ce ƙorafe-ƙorafen basu da tushe bare makama hasalima lokacin wa’adin mulkin da ake ƙalubalantar wato daga 2018 zuwa 2023 ya riga ya ƙare harma an sake gudanar da wani sabon zaɓe.

Ya kuma ce, cigaba da sauraren ƙarar tamkar bata lokaci ne kuma kotuna ba makarantu ba ne da za a riƙa ɓata lokaci wajen dogayen muhawara amma waje ne na sasanta rigingimu tare da yanke hukunci.

A cikin hukuncin kotun ta Amince da ƙudirin Majalisar Zartarwar RTEAN na 2018 da 2019 na amincewa da Musa Mai-Takobi a matsayin halastaccen shugaban ƙungiyar.

Hukuncin kotun ma’aikatar ta tarayya bai gamsar da Eriyo Osakpamwan Wanda yasa ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ta gaba inda ya kalubalanci hukuncin da kotun ta yanke a shekara ta 2020.

Da ya ke jawabi akan hukuncin na Kotun Ɗaukaka Ƙarar, Musa Muhammed Mai-Takobi ya yaba wa hukuncin na kotun wajen aiki tuƙuru tare da tabbatar da gaskiya da adalci inda ya yaba wa ƴaƴan RTEAN a sassa daban-daban na faɗin ƙasar kan nuna haƙuri tare da goyon bayan da suke bai wa shugabancinsa.

Ya bayyana cewa, hukuncin ya tabbatar da gaskiya da wanzuwar tsarin dimukraɗiyya a harkokin cikin gida na ƙungiyar tare da fatan ɗorewar cigabanta da kare muradun illahirin Ma’aikatan Sufuri a Nijeriya.

Ya kuma kirayi fusatattun ƴaƴan ƙungiyar da suka ƙalubalanci jagorancin nasa da su haɗa hannu da shi don ci-gaban RTEAN.

By Babaji