
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozomomi ta Ƙasa, ta sanar da janye yajin aiki na kwana bakwai da ta fara yi bayan cimma matsaya
da Gwamnatin Tarayya.
A ranar Laraba suka tsunduma cikin yajin bayan sun zargi gwamnati da kasa cika alƙawarin ƙara musu albashi da alawus-alawus, da ƙara yawan ma’aikata, da inganta wuraren aiki.
Shugaban ƙungiyar ta National Association of Nigeria Nurses and Midwives (NANNM), Haruna Mamman, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta bayar da umarnin cika akasarin buƙatun nasu.
“Saboda yarjejeniyar da muka cimma da kuma nuna jajircewarmu, mun jingine yajin aikin da muke yi na ƙasa baki ɗaya nan take,” inji shi cikin wata sanarwa daban a yau.
A jiya Juma’a Ministan Lafiya, Muhammed Ali Pate ya ce ƙungiyar ta amince da janye yajin aikin bayan yarjejeniyar da suka ƙulla.
Sanarwar ta nemi mambobin ƙungiyar su koma bakin aikinsu nan take.
