Sarkin Katsina ya amince da naɗa hakimai shida a masarautarsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata sanarwa da ta fito daga sakataren masarautar Bello Mamman Ido(Sarkin Yaƙin Katsina ya ce a cikin sabbin hakiman har da tsohon ministan sufuri sanata Hadi Sirika a matsayin (Durbin Katsina) Hakimin Shargalle.

Akwai Muhammad Dikko Raɗɗa ɗa ga gwamna Dikko Raɗɗa a matsayin (Gwagwaran Katsina) Hakimin Raɗɗa.

Sai Sanusi Kabir Usman (Karshen Katsina)Hakimin Shinkafi da Ahamed Abdulmummuni Kabir Usman (Ɗan wajen Katsina)Hakimin Da kama.

Akwai kuma Abubakar Dardisu (Sarkin Mudurun Katsina) Hakimin Muduru da Gambo Abdullahi Dabai (Dausayin Katsina) Hakimin Dabai.

By ukarofi