2027: Peter Obi na shirin komawa PDP don tikitin takarar shugaban ƙasa – Modu Sheriff

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan jihar Borno, ya yi iƙirarin cewaɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, na kan hanyarsa ta komawa jam’iyyar PDP.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na gidan Talabijin na Channels na Siyasa a Yau.

Obi, tsohon gwamnan Anambra, ya fice daga PDP a ranar 25 ga Mayu, 2022, gabanin zaɓen 2023.

Obi ya bar jam’iyyar PDP kwanaki kafin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa “abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar ba sa goyon bayan ingantacciyar gudunmawa”.

Tsohon gwamnan dai zai halarci zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa ranar 28 ga watan Mayun 2022 kafin ya bar jam’iyyar.

A ranar 27 ga Mayu, 2022, Obi ya shiga jam’iyyar LP, inda ya zama dan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

A halin yanzu dai tsohon gwamnan na Anambra yana cikin haɗakar ‘yan adawa da ke shirin tunkuɗe Shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027.

Gamayyar dai ta amince da jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a matsayin jam’iyyar na tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.

Sai dai kuma burin shugaban ƙasa na wasu mambobin ƙungiyar da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya janyo raɗe-raɗin cewa Obi zai iya ficewa.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV, Modu Sheriff ya yi iƙirarin cewa akwai bayanai da aka samu sun nuna Obi zai koma PDP a kowane lokaci.

Ya ƙara da cewa Obi yana neman lokaci ne kawai kafin ya koma tsohuwar jam’iyyarsa.

“Game da wannan siyasar, ADC ba ta wanzuwa. Ka ba jam’iyyar watanni uku kuma za ta mutu,” inji Sheriff.

“Bayanan da nake da su na cewa a kowane lokaci daga yanzu Peter Obi zai koma PDP ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP.”

By ukarofi