
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya jajenta wa ƙasar Ghana bisa mummunan hatsarin jirgin helikwafta da ya yi sanadin rasa rayukan ƴan ƙasar guda takwas ciki har da ministoci biyu.
Iftila’in ya auku ne da wata helikwafta ƙirar ‘Z-9 helicopter’, wadda mallakar rundunar sojin ƙasar ce da ta taso daga Birnin Accra zuwa Obuasi, ranar Laraba.
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai Ministan Tsaron ƙasar, Edward Boamah da na Muhalli, Ibrahim Mohammed.
Sauran sun haɗa da Muniru Mohammed, mataimakin kodinetan tsaro na riƙo; Samuel Sarpong, mataimakin shugaban jam’iyyar NDC kuma tsohon ministan shiyyar Ashanti; Samuel Aboagye; Peter Twum Ampadu; da kuma Ernest Addo.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Shugaba John Mahama na ƙasar cewa suna tare da su wajen jimamin rashin manyan jami’an, sannan suna yi wa mamatan da ƙasar addu’o’i na musamman game da iftila’in.
Baya ga haka, Tinubu ya jajenta wa iyalai, ƴan uwa da abokan arziƙin waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Ya kuma yi addu’ar samun rahama ga mamatan gami da samun haƙurin juriya rashin su ga makusantansu.
