Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bai wa jami’an tsaro umarnin Kamo duk wanda yake da hannu a sanadiyyar mutuwar hadiminsa Sadiq Gentle.
“Ina matuƙar alhini game da rasuwar Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman a ma’aikatar tarihi da al’adu ta Jihar Kano, wanda ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a wani mummunan harin da wasu da ake kyautata zaton ƴan daba ne suka kai a baya-bayan nan”.
A cikin saƙon ta’aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa Manhaja Blueprint, gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Gentle a matsayin “ƙwararre mai kishin al’umma a kafafen sada zumunta” wanda mutuwarsa ta tashin hankalin gwamnatin jihar da kuma kafafen sada zumunta.
“Na yi matukar baƙin ciki lokacin da na sami labarin rasuwar Malam Sadiq Gentle,” in ji Gwamnan.
Gwamna Yusuf ya yi Allah-wadai da kisan da kakkausar murya, yana mai bayyana shi a matsayin “mummunan abun da ba za a amince da shi ba.”
Sannan Gwamnan ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan Gentle da abokan arziki da kuma abokan aikinsu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar Kano za ta kasance da su a wannan mawuyacin yanayi.
