Luguden wuta: Sojojin sun tilasta ‘yan bindiga sakin basarake a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A wani gagarumin farmakin da rundunar sojin saman Nijeriya ta kai na yaƙi da masu aikata laifuka, rundunar sojin saman Nijeriya ta ƙaddamar da wani samame ta sama kan wasu ‘yan bindiga da suka ɓoye a ƙauyukan tsaunin Yankuzo da ke ƙaramar Hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Hare-haren da aka ci gaba da kai wa ya ji wa ‘yan ta’addan mummunar rauni, wanda ya tilasta musu barin maɓoyarsu.

Sahihan bayanan sirri da ci gaba da sa ido ta sama sun bayyana tarin ‘yan bindiga da ke tafiya cikin ƙungiyoyi da nufin kai hare-hare kan al’ummomin da ke yankin. Da yake aiki da wannan bayanan, NAF a ƙaƙkashin Operation FANSAN YAMMA, sun aiwatar da aikin haɗin gwiwa, tare da kawar da barazanar da dama tare da daƙile yunƙurin maharan.

A ranar da aka kai harin ta sama, Manhaja ta tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun sako basaraken gargajiya na Yankuzo, Alhaji Babangida Kogo. A baya dai an kama sarkin ne da wasu ‘yan bindiga masu tuƙa babur da ke gudanar da ayyukansu.

Ana kyautata zaton sakin sarkin ya biyo bayan matsin lambar da sojojin ke yi na yaƙin sama tare da goyon bayan sojojin ƙasa, wanda ya tilastawa ‘yan ta’adda tserewa tare da yin watsi da waɗanda suka kama. Wannan ya nuna gagarumin ci gaba a yaƙin da ake da ‘yan fashin a ƙauyuka a Zamfara.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan bindiga sun kashe mahaifin Alhaji Kogo, tsohon Hakimin Yankuzo, a daidai wannan hanya shekaru biyu da suka gabata—wani lamari mai ban tausayi da ya nuna ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a yankin.

By ukarofi