Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa, an ƙayyade Naira Miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin aikin Hajjin 2026.
Hukumarr NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis da maraice, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar bakiɗaya, don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an ƙayyade miliyan N8.5 ɗin ne a matsayin kafin alƙalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙaƙanin kuɗin.
Ya ce, Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.
Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Nijeriya, inda ya ce ƙoƙari da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin sauƙaƙa musu.
Ya kuma amince da shigar da Gwamnatin Tarayya ta yi na ba da damar biyan kuɗin Hajji a Naira, manufar da ta taimaka wajen kare alhazai daga taɓarɓarewar kasuwar canji a lokacin aikin Hajjin 2025.
A wajen taron bayan hajjin, an gudanar da muhimman tantaunawa dangane da tsare-tsare na lokaci, kwangilolin jiragen sama, da kuma daidaita kayan aiki na ayyulan da ke tafe.
Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike da ƙididdiga da Bayanai (PRSILS), Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, ya gabatar da kalandar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya zayyana lokutan tashi, balaguro, da dawowa, tare da wa’adin da hukumar gudanarwar jiha ta ɗauka da rajistar maniyyata.
Aikin Hajjin shekarar 2025 ya fuskanci aalubale da dama da suka shafi kayan aiki da gudanarwa, waɗanda aka tattauna da yawa a yayin taron bayan hajjin.
