Daga ABDUSSALAM ABUBAKAR NASIDI
A da, duk lokacin da aka samu rikici ko tarzoma da suka shafi ’yan daba a Kano, yatsar zargi na nuni kai tsaye ga gwamnati. Ana cewa, gwamnati ce ta kasa. Sai dai a yanzu, wasu al’umma a cikin wannan sabon salo na faɗan daba da ke faruwa kusan kullum a unguwanni da dama, an fara ɗora alhakin ne kan iyaye da tarbiyyar gida. To, amma gaskiyar magana ita ce: Shin iyaye kaɗai ne ke da laifi? Ina rawar da gwamnati za ta taka a cikin wannan rikicin da ke ƙara ƙarfi?
A da siyasa da ‘yan daba hannu ɗaya ne:
Kafin dawowar Gwamna Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso a 2011, yawancin ‘yan siyasa da masu riƙe da madafun iko a Jihar Kano sun ɗauki ’yan daba a matsayin kayan aiki. Sun ba su mafaka a gidajensu, sun riƙa musu riƙon ’yan amana, wasu ma har kuɗi da alawus ake ba su, don tsoratar da abokan hamayya a siyasa. A wancan lokacin, siyasa da daba tamkar hanta da jini ne.
Sauyin da aka fara gani a 2011:
Da Kwankwaso ya hau mulki a karo na biyu, ya bijire wa wannan mummunar al’ada. Ya daƙile amfanin ‘yan daba a harkokin gwamnati da siyasa. Wasu daga cikin matakan da gwamnatin sa ta ɗauka sun haɗa da:
*Kafa makarantar gyaran hali ta ƙiru, inda aka riƙa tura matasa masu ɗabi’ar daba, don koya musu sana’a da tarbiyya.
*Samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar koyar da sana’o’i da raba kayan aiki. A wannan lokacin aka samar hukumar KAROTA da ɗauykar masu gadin makarantu da ma’aikatu, inda aka ɗauki da yawa daga masu wannan ɗabi’a da aka gyara.
*Hana shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi tare da kafa tsaruka masu tsauri a kai.
*Daƙile ɗaukar belin masu laifi, musamman ’yan daba da masu laifi na gari. Wannan lokacin waɗanda ba za su iya ba, barin garin suka yi suka gudu, saboda matsi, waɗanda kuma suka yi tauri, an tura su gaba da suka gagara.
Wannan tsari ya taimaka wajen rage faɗan daba a jihar. A lokacin, ’yan daba sun rasa mafaka, sun rasa ƙwarin gwiwa, kuma an bar su a cikin fargaba da firgici.
Komawar Matsala: Siyasa ta ƙara tsoma baki:
Amma daga 2019 zuwa yau, al’amura sun fara sauyawa. Yayin da siyasa ta fara ƙaratowa, aka fara fitowa da tsofaffin ’yan daba daga gidan yari da nufin su zama kayan aiki a yaƙin neman zaɓe. Wannan ya janyo komawar salon tsohon daba, amma a karo na biyu, sun fi muni da hatsari. A yanzu ba wai faɗa kawai ake ba, har da sace kaya, fashi da makami, raunatawa ko kisa.
Tambayoyi da dole a duba:
*Shin iyaye ne suka tilasta wa gwamnati ta kasa samar da ayyukan yi?
*Shin iyaye ne ke raba miyagun ƙwayoyi a kasuwannin cikin gari da dare?
*Shin iyaye ne ke ɗaukar nauyin belin ’yan daba daga hannu hukumomi banda ’yan siyasa?
*Me gwamnati ke yi, don daƙile yaɗuwar ta’addanci da faɗan daba a unguwanni?
Gaskiyar al’amari:
Kamar yadda iyaye ke da haƙƙin tarbiyyar ’ya’ya, haƙƙoƙin gwamnati sun fi nauyi wajen kafa tsari, samar da aiki, daƙile ƙwaya da tabbatar da tsaro. Idan gwamnati za ta hana ɗaukar belin ’yan daba, ta tsaurara tsaro a kasuwar ƙwaya, ta kafa cibiyoyin gyaran hali, ta riƙa tsare masu laifi yadda ya kamata, faɗan daba zai ragu matuƙa.
A ƙarshe lokaci ya yi da gwamnati za ta yi abin da ya dace:
*ɗora laifi kan iyaye kaɗai wani salon kauce wa alhakin gwamnati ne. Iyayen ba su da ikon hana faɗan daba muddin gwamnati ba ta tashi tsaye da cikakken shiri da tsarin doka ba.
*Gyaran al’umma aiki ne na haɗin gwiwa; iyaye, malamai, shugabannin al’umma da gwamnati — amma gwamnati ce ke kan gaba wajen ɗaukar nauyi.
Nasidi – ɗan Kishin Kano – ya rubuto ne daga unguwar Gwangwazo a ƙaramar Hukumar Birnin Kano da Kewƙaye da ke Jihar Kano
2 ga August, 2025
