Daga ABDULLAHI MOHAMMED
A duniyar siyasa da iko, shakku da jita-jita su ne kuɗin musayar tasiri, yayin da labaran da aka ƙirƙira sukan zama makaman hallaka mutuncin abokan hamayya. A kwanakin nan, sunan Bashir Bayo Ojulari, Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ya shiga sahun waɗanda ake yawan hasashe da jita-jita marasa tushe akansu.
Rahoton da gidan jaridar TheCable ta fitar da’awar “na musamman” ba ya da kamannin bincike na gaskiya, illa dai tamkar hukunci da aka ɗora masa kwalliya ta aikin jarida ne. A cikin saƙonsa, rahoton na ƙoƙarin nuna cewa, kwanakinsa a ofis sun ƙare, saboda alaƙar aiki da ya yi da Abdullahi Bashir-Haske, wani mai kamfani da ke da alaƙa da ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa. Amma idan aka dubi lamarin da idon adalci, babu wani laifi da aka tabbatar da Ojulari ya aikata, kuma babu dokar da ya karya.
Wannan irin jita-jitar tana ƙoƙarin zana shi da kwatankwacin “maɗaukakin mai cin amana,” saboda kawai ya yi hulɗa da wani mai kamfani wanda matarsa ’yar wani fitaccen ɗan siyasa ce. A wannan ƙasar da kowa ke da alaƙa da wani, ko dai ɗan uwa ne, makwabci, abokin makaranta ko kuma tsohon abokin aiki, za mu rushe tushen ci gaban ƙasa idan hƙr muka fara ganin dangantakar dangi a matsayin laifi.
Ojulari bai hau kujerar shugabancin NNPC don ya yi wa wata ƙungiya biyayya ba, ko don ya raira wa wata jam’iyya waƙa ba. An zaɓe shi ne saboda ƙwarewarsa da fahimtarsa tsakanin fasahar duniya da tsarin cikin gida. Tun lokacin da ya hau kujerar, ya kawo sabbin hanyoyin aiki da suka maye gurbin ƙazamin tsohon tsarin da ya dogara da son zuciya da ’yan fassara.
Ya karɓi ragamar NNPC a wani lokaci mai sarkakiya, bayan aiwatar da Petroleum Industry Act, bayan komawar NNPC kamfani, kuma bayan juyin ra’ayi na yarda da kamfanin daga al’umma. Amma maimakon ya tsaya don ya yi kallo, ya fuskanci tsofaffin matsaloli kai tsaye: ya fara bincike, rage almubazzaranci, ya sake fasalin tsarin aiki, kuma ya janyo gwiwar jama’a wajen ganin NNPC ta tashi daga duhu zuwa gaskiya.
Duk da haka, wannan gyara ya shiga kunnen waɗanda suka dogara da tsohon tsarin na almubazzaranci da cin hanci. Su ne waɗanda ke ta fitar da ƙagaggun labarai da nufin jefa Ojulari cikin ruɗani. Amma kamar yadda fitaccen ɗan falsafa Plato ya ce, a tatsuniyarsa ta kogon duhu, waɗanda ke cikin duhu sukan ƙi wanda ya fita ya ga haske. Ojulari, da alama, ya zama irin wannan mutum da ya ɗauki haske, wanda wasu ke ƙoƙarin dawo da shi cikin duhu.
Idan da gaske ana tuhumar laifi, to me ya sa babu wata ƙara da aka kai kotu? Kuma ko da hukumar EFCC na bincike ne, ba laifi ba ne hakan, me ya sa aka ɗauki hakan a matsayin hukunci kai tsaye? Muna rayuwa a ƙasa da ake ɗaukar jita-jita a matsayin hukunci. Wannan ba adalci ba ne, fitina ce da aka ɗaure mata gindi da alama.
Kasancewar kamfanin AA&R Inɓestment Group yana hulɗa da NNPC tun kafin zuwan Ojulari ya isa ya rusa dukan ginin da ake ƙoƙarin ginawa na zargi. Ko da kuwa mamallakin kamfanin yana da dangantaka da iyalan wani ɗan siyasa, hakan ba ya nufin an karya doka ba. Idan wannan ne kuskure, to babu wata hulɗa da za ta tsira a Najeriya.
Abin damuwa ma shi ne, yadda aka mayar da jita-jitar binciken EFCC zuwa hukuncin laifi. Har yanzu babu wata ƙara da aka shigar gaban kotu, balle a samu hukunci. Amma labaran da suka ginu akan “ana binciken shi” sun bazu fiye da labaran da suka nuna nasarorin da ya samu. Wannan salon “kisa ta kafar jarida” yana mayar da ƙasar nan ta zama wuri da ba za a iya gudanar da sauyi ba.
A gaskiya, tarihin Ojulari ya fi kowace jita-jita magana. Daga jagorancinsa a SNEPCo har zuwa shigar da sabbin tsare-tsare a NNPC, ya nuna cewa cancanta ce ta kawo shi, ba siyasa ba. Ya yi alƙawari ga ƙasar nan, ba ga wata ƙungiya ko wata alaƙa ba.
Waɗanda ke ƙoƙarin zubar da mutuncinsa ba sa ƙoƙarin kare Najeriya, suna kare kansu ne daga sauyin da ya kawo. Ojulari na matuƙar barazana ga tsarin da ya zamo hanyar amfana ba bisa ƙa’ida ba. Kuma saboda haka ne suka koma ɓoyayyun ƙoƙari da ɓata suna, da fatan za su gaji da karfin bin gaskiya.
Ya kamata mu sani cewa, Najeriya ba ta da sarauta da ke gina kan aminci ko soyayya kawai. Najeriya ƙasa ce ta doka, kuma dokar ta ce ya kamata ta yi jagora, ba hayaniya da jita-jita ba.
Bashir Bayo Ojulari bai cancanci wannan harin na sharri ba. Cancanta da gyaran da ya kawo su ne ya kamata su zama abin yabawa, ba abin suka ba. Lokaci ya yi da za mu kare ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da ƙwazon aiki, ba mu yarda da ruɗin masu son komawa tsarin da ba ci gaban ƙasa ba.
A ƙarshe, Ojulari ba matsala ba ne, mafita ne. Kuma idan muka ƙyale a rugurguje shi da ɓoyayyun magana da hasashe marasa tushe, za mu tabbatar da abin da tarihi ya daɗe yana nuna mana: cewa Najeriya ƙasa ce da ke ƙin canji, amma tana kuka da rashin ci gaba.
ƙima na da rauni, aminci ma haka. Amma a rubuta cikin tarihi: inuwa ba ta iya gurbata rana. Ojulari yana tsaye ba saboda shi cikakke ne ba, amma saboda ya zaɓi yin abin da ya dace. A irin wannan lokaci, yin daidai abin tsoro ne. Shi ya sa ake jin tsoron sa.
Amma gaskiya za ta bayyana. Tarihi zai bayyana wane ya yi gaskiya da wanda ya nemi hana canji. Rana ta kusa bayyana. Kuma in har muka bar wannan ɗan Najeriya mai ƙwazo ya faɗi, to ba saboda ya gaza ba ne, saidai saboda ya ƙi gazawa a gaban marasa kishin ƙasa.
A bar Ojulari ya yi aikinsa. A bar gaskiya ta ci nasara. A bar rana ta fito.
Mohammed ya rubuto ne daga Abuja
