Kuwait ta bai wa Nijeriya rancen Dala miliyan 25.35 don magance rashin zuwa makarantar yara a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar rance mai rangwame na dala miliyan 25.35 da Asusun Raya Tattalin Arzikin Larabawa na Kuwait domin tallafawa shirin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kaduna.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa rancen, wanda aka sanya hannu a madadin Jihar Kaduna, na cikin ƙunshin kuɗi na dala miliyan 62.8 da haɗin gwiwar abokan ci gaba na ƙasa da ƙasa, da nufin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ga yara marasa galihu.

Sanarwar da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta bayyana cewa kuɗin zai tallafawa shirin “Reaching Out-of-School Children”, wanda zai bai wa fiye da yara 100,000 damar shiga makaranta, tare da gina sababbin makarantu 102 da gyara 170 a yankunan da ke da buƙata.

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce shirin na nuna aniyar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya da auna sakamako a ɓangaren saka hannun jari na ilimi, tare da yabawa Jihar Kaduna da yadda ta cika wajibinta da gudummawar dala miliyan ɗaya.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa jihar ta ware kashi 26 na kasafin kuɗinta na shekarar 2025 domin ilimi.

Sauran abokan haɗin gwiwa sun haɗa da Bankin Raya Musulunci (IsDB), GPE, Education Aboɓe All Foundation da Saɓe the Children.

Za a sa ido kan aiwatar da shirin ta hanyar duba yawan ɗalibai, horar da malamai da kuma ingancin koyo, domin tabbatar da sakamako mai ɗorewa.

By ukarofi