Mun fara shirin farfaɗo da masaƙun Kaduna don inganta tattalin arziki – Ministan Masana’antu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da wani shiri na farfaɗo da masana’antun auduga, masaƙu da tufafi a ƙasar, inda ƙaramin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Enoh, ya kai ziyara jihar Kaduna domin duba muhimman masana’antun da suka shafi ɓangaren.

Ministan ya bayyana cewa sake farfaɗo da waɗannan masana’antu zai taimaka matuƙa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa da samar da ayyukan yi ga matasa da ma sauran ’yan ƙasa.

Bayan gudanar da wannan ziyara ta gani da ido, Sanata Enoh ya halarci wani taro tare da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da martabar masana’antun sarrafa auduga da samar da tufafi a Nijeriya. 

Ya jaddada muhimmancin sake farfaɗo da kamfanin United Nigerian Textiles Limited (UNTL) da ke Kaduna, yana mai cewa hakan zai ƙara wa masana’antun masaku ƙwarin gwiwa da kuma farfaɗo da harkokin masana’antun gaba ɗaya.

A nasa jawabin a yayin taron, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwa rsa kan yadda masana’antar UNTL ta tsaya cak tun shekarar 2022, inda ya danganta haka da taɓarɓarewar tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

Yana mai bayyana cewa masana’antar na da tarihin samar da fiye da guraben ayyukan yi dubu goma (10,000) a fannoni daban-daban, kafin durƙushewarta.

By ukarofi