Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ma’aikatan hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomin jihar Nasarawa da ake kira Nasarawa State Local Goɓernment Service Commission a Turance, sun yaba wa sabon shugabansu na hukumar wato Abdullahi Mustapha Aliyu dangane da tsarinsa na musamman na tabbatar da cigaban hukumar kawo yanzu da zuwansa kujerar wata biyu kacal.
Ma’aikatan hukumar sun bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar neman rahoto na musamman da wakilinmu ya kai sakatariyar hukumar a fadar gwamnatin jihar wato Lafiya a mako da ake ciki.
Sun ce zuwa yanzu cikin watanni 2 kacal akwai wasu ingantattun tsare-tsare da shugaban hukumar Abdullahi Mustapha Aliyu ke cigaba da ƙirƙirowa da dama dake daga darajar hukumar tare da shirya horo da hanyoyin sanin makamar aiki da sauransu da yake samar musu da hakan ya bambanta shi da sauran tsafaffin shugabannin hukumar da suka gabata.
Ma’aikatan hukumar dake kula da harkokin duka ƙananan hukumomin jihar da aka zanta da sun kuma bayyana cewa cewa naɗin sabon shugaban nasu Abdullahi Mustapher Aliyu zaɓi ne nagari kana suka yi amfani da damar inda suka yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da zaɓin ƙwararren shugaban.
Sun ƙara da cewa shugaban yakan kuma zama da su na musamman akai-akai inda yake binciko ƙalubalai dake fuskantar kowanne fannin hukumar tare da samar da mafita ba tare da ɓata lokaci ba.
Daga ƙarshe sai ma’aikatan duk suka taya sabon shugaban nasu Abdullahi Mustapher Aliyu murnar naɗin nasa tare da buƙatarsa ya cigaba da kyakkyawar aikin da yake gudanarwa don cigaban hukumar da ma jihar bakiɗaya.
A ‘yan kwanakin baya ne dai gwamnan jihar ta Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa tare da rantsar da sabon hukumar na harkokin ƙananan hukumomin jihar wato Abdullahi Mustapher Aliyu wanda kwarerren ne da ya rike mukamai dabandaban da dama a jihar dama ƙasa baki ɗaya a matsayin sabon shugaban hukumar.
