2027: Abinda ya sa Jonathan ya fi cancantar tsayawa takara a PDP – Sule Lamiɗo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya bayyana tshohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Johnathan a matsayin babban zaɓin jam’iyyar PDP a zaɓen 2027 da ke tafe, yana mai kira a gare ta da ta yi ƙoƙarin dawo da shi cikinta.

Lamiɗo ya bayyana haka ne yayin hira da gidan telebijin na Channels a ranar Juma’a inda ya ce duk wanda jam’iyyar ta tsayar, ƴan Nijeriya za su ba shi goyon baya.

Ya ce, a matsayin Jonathan na wanda ya taɓa jagorantar ƙasar a baya, ya fahimci shugabanci kuma yi aiki da kyau da sauran ƴan siyasa, babu wani mamban jam’iyyar daga kudu da ya kai shi ƙwarewa.

Akan haka ne ya ce yana maraba da shi zuwa jam’iyyar a matsayinsa na wanda ya fi cancanta matuƙar ya amsa kiransu.

Haka kuma, Lamiɗo ya yi kira da a tilasta wa Ministan Abuja Nyesom Wike barin jam’iyyar; da tsohon gwamnan Benuwai Samuel Ortom; da tsohon gwamnan Abia Okezie Ikpeazu da wasu mambobinta da a cewarsa, sun yi jam’iyyar zagon-ƙasa a zaɓen 2023.

Jigon jam’iyyar PDP’n ya kuma koka da halin rashin ladabtarwa da jam’iyyar ke fama shi, lamarin da ke haifar mata da koma-baya a harkokinta, yana mai kira da a ɗauki matakin hukunta duk wanda aka samu da laifin saɓa wa dokokinta.

By Babaji