Kano: Za mu shirya wa mazauna gidan gyaran hali da gidan yaran Nassarawa wa’azi – Hukumar Shari’a

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano za ta shirya wa mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Janguza da gidan yara na Nassarawa, Wa’azi, domin faɗakar da su akan gyaran tarbiyya.

Shugaban hukumar Shari’ar a nan Kano Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya bayyana hakan a lokacin da hukumar ta ziyarce gidan gyaran hali na Janguza, a Larabar nan, domin ƙara ƙulla alaƙar aiki, a wani ɓangare na cika umarnin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, wajen ragewa mazauna gidajen wani raɗaɗi.

Hukumar Shari’ar ta kuma ziyarci gidan gyaran hali na Goron Dutse, da gidan kula da yara na Nassarawa, da na kula da masu taɓin hankali na Tudun Maliki, inda ta bai wa mazauna gidajen tallafin dafaffen abinci da lemu da ruwa, da kuma kayan marmari, irin su lemun zaƙi da kankana da abarba, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani game da ziyarar da suka kai, Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano Sheikh Ali Dan’Abba, ya ce sun kai ziyara gidajen ne domin tallafawa mazauna gidajen, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta ƙarfafa zaman lafiya a jihar Kano.

Da yake nasa jawabin shugaban gidan ajiya da gyaran hali na Janguza DCC ɗanlami Inuwa, ya ce tallafin dafaffen abincin na mutum 400, da lemu da ruwa, da hukumar Shari’ar ta bai wa mazauna gidan abin a yaba ne, har ma ya yi kira ga sauran al’umma da su rinƙa ziyartar gidajen domin tallafawa ɗaurarru.

Shi ma a nasa ɓangaren, mataimakin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali a nan Kano, kuma mai kula da gidan na Goron Dutse AC Kafilu Abdullah Nassarawa, miƙa godiyarsa ya yi bisa ziyarar da hukumar ta kai musu.

A yayin ziyarce-ziyarcen gidajen gyaran halin na Janguza da na Goron Dutse, da gidan kula da Yara na Nassarawa, da kuma gidan kula da masu taɓin hankali na Tudun Maliki, shugaban hukumar Shari’ar ta jihar Kano Sheikh Abbas Abubakar Daneji, yana tare da Kwamishina na ɗaya a hukumar Gwani AbdulHadi Dahiru Yakasai, da na biyu Sheikh Ali Dan Abba, da daraktoci, da sauran ma’aikatan hukumar.

By ukarofi