Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), sun kama wasu kayayyaki na hodar iblis da tramadol mai nauyin kilogiram 225 da aka ɓoye a cikin madubin mota guda 71 domin safarar zuwa birnin Libreɓille na ƙasar Gabon.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Babafemi ya bayyana cewa, an yi jigilar magungunan ne ta wurin da ake fitarwa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, Ikeja Legas.
Ya ce, an riga an kama mutane aƙalla uku da ake zargin su na da hannu a cikin wani samame da aka yi musu.
‘Kashi na farko na kayan da ke ɗauke da ƙwayoyin Tramadol 57,420 da hodar iblis 57 mai nauyin kilogiram 1.60 an kama su a cikin wani kaya da zai je Gabon a Air Cote d’Iɓoire a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli.
“Ba tare da ɓata lokaci ba aka damƙe wani fitaccen wakilin dakon kaya Ihekweme Osinachi da ke kula da jigilar kaya, bayan da aka ci gaba da bincike har aka kama wani wanda ake zargi Uzochukwu Chukwurah a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli.
“An gano fakiti 11 na hodar iblis da nauyinsu ya kai kilogiram 1 daga baya daga wasu madubi guda huɗu da ake shiryawa don fitar da su a gidan Uzochukwu a ranar Litinin, 21 ga watan Yuli.
“Wannan ya kawo jimlar adadin hodar iblis zuwa 68 masu nauyin kilogiram 2.60,” inji shi.
A wani labarin kuma, Jami’an NDLEA a ranar Juma’a, 1 ga watan Agusta sun kama wata ‘yar kasuwa Rosanna Nwafor a shagonta da ke cikin rukunin kasuwanci da ke Ojo, Legas.
Babafemi ta ce, kama ta ya biyo bayan kama kilogiram 100 na hodar iblis da kilogiram 300 na kwayar phenacetine.
Wannan, inji shi, wani sinadari ne, wanda aka ɓoye a cikin robar man baki na mata da ke zuwa Malabo, Eƙuatorial Guinea, ta hanyar fitarwa ta filin jirgin saman Legas a ranar 10 ga Yuli.
“An kama jami’an jigilar kaya guda biyu da ke da alaƙa da jigilar kayayyaki tun da farko kafin a kama Nwafor wadda ke gudanar da sana’ar ta’addanci a matsayin sana’ar iyali tare da mijinta Remigus Nwafor, a halin yanzu.
“A cikin bayanin da ta yi, Nwafor ta yarda cewa ta sayi lipsticks da aka yi amfani da su don ɓoye haramtattun ƙwayoyi yayin da mijinta ke kula da ainihin kayayyakin kwayar,” inji shi.
