Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a Jihar Kano sun bayyana goyon baya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓe na biyu a 2027, tare da tabbatar da biyayyarsu ga jagoran jam’iyyar a Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sun bayyana goyon bayan ne a taron masu ruwa da tsaki na musamman da ya gudana a ranar Talata a gidan Ganduje da ke Kano.
Taron ya mayar da hankali ne kan haɗin kan jam’iyya, shirin zabe mai zuwa, da kuma ci gaban da gwamnatin Tinubu ke samu a Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano.
Da ya ke jawabi a taron, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa taron an shirya shi ne domin warware wasu matsalolin cikin gida, ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar, da kuma shiryawa jam’iyyar tsaf domin fuskantar ‘yan adawa a zaɓen da ke tafe.
“Muna masu nuna cikakken goyon baya ga nasarar Shugaba Tinubu da kuma jam’iyyarmu mai girma.
“Wannan taron mun kira shi ne da nufin ƙarfafa tushenmu, ƙarfafa haɗin kai, da kuma shirya APC domin samun nasara a zaɓukan 2027.”
