Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakan gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a ƙananan hukumomin Matazu da Sabuwa da wasu sassan Jihar Katsina.
A yayin zaman majalisar wanda shugaban majalisa Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya jagoranta, ‘yan majalisar sun kuma buƙaci a ƙara jami’an tsaro a ƙaramar hukumar Sabuwa, musamman a Tashar Bawa da sauran wuraren da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a faɗin jihar.
Hon. Ibrahim Umar Dikko, mai wakiltar Matazu kuma babban mai tsawata wa na majalisa, da Hon. Ibrahim Danjuma Machika mai wakiltar ƙaramar hukumar Sabuwa suka gabatar da wannan ƙudiri a zauren majalisar.
Hon. Dikko ya bayyana matuƙar damuwarsa game da ƙaruwar hare haren yan bindiga a Matazu, inda mutane da yawa sun rasa rayukansu da matsugunansu, wasu ma ba sa iya noma saboda barazanar ‘yan bindigar.
Duk da cewa ɗan majalisar ya yabawa gwamna a kan ƙoƙarin da yake a wannan fanni, ya jaddada cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ƙara matsa ƙaimi domin shawo kan taɓarɓarewar tsaron.
Hakazalika, Hon. Machika ya nuna damuwarsa game da janyewar ba zato ba tsammani na jami’an tsaro daga al’ummomin Sabuwa, wanda ya bar su babu kariya daga hare-haren yan bindiga a yankin.
‘Yan Majalisar ƙananan hukumomin Funtua, Ɗandume, Bakori, Kankia, Jibia, Dutsinma, da Ƙafur sun goyi bayan ƙudurorin, inda suka buƙaci a ɗauki matakan gaggawa daga gwamnatin jiha da ta tarayya.
Kakakin majalisar Rt Hon Nasir Yahaya Daura ya baiyana matsayar majalisar a kan waɗannan ƙudurorin, inda ya yi kira ga gwamantin jiha da hukumomin tsaro da su ƙara sojoji a yankunan da ke fama da rashin tsaron, su kuma bincika dalilin janyewar jami’an tsaron a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Haka kuma ya buƙaci gwamnatin jihar ta inganta haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro don maido da zaman lafiya a faɗin jihar nan.
