Gwamnatin Katsina ta shirya yaƙi da rashin abinci mai gina jiki na yara da mata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana sabon shirin haɗin gwiwa da ƙulla dabarun ɓangarori da dama domin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da ke addabar yara da mata a jihar.

Shugaban hukumar kula da lafiyar matakin farko ta jiha, Dakta Shamsuddin Yahya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Katsina.

Ya ce rashin abinci mai gina jiki na daga cikin manyan matsalolin lafiyar jama’a, kuma yana daga cikin manyan dalilan mutuwa da rashin lafiya a jihar.

Ya ce rahoton da ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar kan yawan mace-mace a wata cibiyar kula da yara masu tsananin rashin abinci mai gina jiki, ya zama kira na farga ga kowa maimakon su ɗauke shi a matsayin suka.

“Ba mu ɗauki rahoton a matsayin ƙorafi ba, sai dai kira ne ga kowa ya haɗa kai domin magance matsalar, wadda ta samo asali daga dalilai masu zurfi na zamantakewa da tattalin arziki,” in ji shi.

Dakta Yahya ya bayyana cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta bayar da gudummawar kuɗi ga UNICEF naira miliyan 200 a shekarar 2023 da naira miliyan 300 a shekarar 2024 domin samar da kayan abinci mai gina jiki, wanda UNICEF ta ninka kuɗin a kowace shekara.

Tun daga shekarar 2016, an raba tallafin naira 250,000 a kowane wata ga ƙananan hukumomi 14 da aka tantance a matsayin masu matukar buƙata, don kula da cibiyoyin warkar da yara a wajen asibiti. Haka kuma, dukkan ƙananan hukumomi 34 sun rattaba hannu kan yarjejeniya da za su bayar da naira miliyan ɗaya a kowane wata domin yaƙar matsalar.

A halin yanzu, Katsina na da cibiyoyi 185 na kula da yara a wajen asibiti (OTP) da kuma cibiyoyi 17 na kwantar da marasa lafiya masu tsananin rashin abinci mai gina jiki, inda gwamnati ke kula da fiye da rabin waɗannan cibiyoyi.

Dr shamsuddeen ya bayyana shirye-shirye da dama da gwamnati ke yi wajen samar da abinci, ciki har da rarraba kayan aikin noma, samar da cibiyar injinan noma, da kuma sa ido a kasuwanni domin hana ɓoye abinci.

Sai dai ya bayyana damuwa kan yadda wasu iyaye ke sayar da abincin magani (RUTF) bayan sun karɓa daga cibiyoyi, maimakon su yi amfani da shi wajen warkar da ‘ya’yansu.

” A kan haka ne gwamnati za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta masu laifi da kuma ƙarfafa tsarin kulawa,”Dr shamsuddeen ya faɗi haka.

Masana daga UNICEF, MSF, ALIMA, World Food Programme, da wasu ma’aikatu sun samar da tsari na ɓangarori da dama domin yaƙar matsalar, wanda ake jiran amincewar gwamna.

Dakta Yahya ya ce shirin zai shafi ɓangaren kiwon lafiya da kuma gyaran al’adu, musamman batutuwan tazarar haihuwa da kuma kin amincewa da rigakafin cututtuka, waɗanda ke jawo matsalar ta tsananta.

Shima shugaban shirin Accelerating Nutrition Results in Nigeria (ANRiN) a Katsina, Dakta Umar Bello, ya ce shirin ya kai wa fiye da mutane miliyan uku agaji a dukkan mazaɓu 361 na jihar, ta hanyar ba da Vitamin A, micronutrient powders, iron folic acid, magungunan zazzaɓin cizon sauro ga mata masu juna biyu, da kuma zinc ga yara masu fama da gudawa.

Ya ƙara da cewa, sama da ma’aikatan lafiya 1,000 aka horas kan ilimin kiwon lafiyar uwa da jariri, domin wayar da kan iyaye kan muhimmancin shayar da jarirai nono na tsawon watanni shida, fara ciyarwa daidai lokacin da ya dace, da kuma amfani da hanyoyin tazarar haihuwa.

Ya ce a cikin shirin ANRiN 2.0 da zai biyo baya, Katsina za ta ci gaba da matakan rigakafi tare da raba RUTF ga yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki, ƙarƙashin tallafin Bankin Duniya, yayin da gwamnati ta ware naira miliyan 700 domin ɗorewar shirin.

“Gwamna ya ƙuduri aniyar ci gaba da rigakafi da kuma magance matsalar da ta riga ta faru, tare da haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki domin kare lafiyar mata da yara a jihar,” in ji Dakta Bello

By ukarofi