Daga JOHN D. WADA a Lafia
Sarkin Sharifai na Jihar Nasarawa Prof. Engr. Muhammad Sani Haruna yayi kira na musamman ga iyaye a ƙaramar hukumar Keffi da Jihar Nasarawa baki ɗaya su tabbatar suna turo ƴaƴansu neman ilimin addini da na zamani a makarantar Al’mumtaz da ke birnin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar.
Prof. Haruna wanda tsohon shugaban hukumar kimiya da fasaha da kuma ayyukan cigaba na ƙasa wato National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI) a turance ne kuma har iya lau dan takaran kujerar gwamnan Jihar Nasarawar ne a shekarar 2027 dake tafe a inuwar jam’iyyar APC yayi wannan kira ne a jawabinsa yayin da ake gudanar da bikin gabatar da wasiƙun shedar kammala karatu da kyaututtuka na musamman wadda makarantar Al’mumtaz ɗin ta shirya ta kuma gabatar a babban filin taron babbar jami’ar jihar a ƙarshen makon da ya gabata.
Ya ce wannan kira ya zama dole ne domin makarantar ta Al’mumtaz ta bambanta da saura a fannin samar da ingantaccen ilimi da ɗabi’a.
Ya kuma yaba wa ƴaƴan makarantan na Al’mumtaz ɗin da suka kammala karatu da kyaututtuka na musamman da suka samu yana mai cewa su ne jakadun makarantar kuma su ci gaba da burge iyayensu.
A nasa ɓangaren da yake jawabi shugaban makarantar Dr. Musa Ahmad Isah ya gode wa duk wanda ya halarci taron musamman sarakunan gargajiya musamman mai martaba sarkin Keffi ALH. Dr. Shehu Chindo Yamisa da a a cewar sa suke cigaba da bada gagaruman gudumawa da cikakken goyon bayan su ga makarantar tun farkon kafa ta.
Ya kuma yaba wa iyayen yaran a kan sadaukarwar su wajen ba ƴaƴansu mafi kyawun ilimi, yana mai jaddada aniyar makarantar ta Al’mumtaz na cigaba da waɗannan kyawawan ayyukan samar da ilimin addini dana zamani wa al’ummar yankin da na jihar baki ɗaya.
Abubuwa da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da gabatar da wasannin kwaikwayo mai ɗauke da sakonnin rayuwa daga ɗaliban makarantar da bai wa wasu manyan baƙi lambobin yabo na musamman da sauran su.
