Abinda masu tambayoyi a EFCC suka faɗa mun – Tambuwal bayan fitowa daga hannun hukumar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya magantu game da haɗuwarsa da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, inda ya bayyana cewa babu wani matsin a siyasance ko daga wata cibiya da za ta tsorata shi.

Da yake jawabi ga manema labarai a Sakkwato bayan fitowarsa daga komar EFCC, Tambuwal ya ce ganin sa a ofishin hukumar ya faru ne sakamakon gayyatar da ta yi masa a ranar 6 ga watan nan na Agusta.

Ya ce, bayan ganawa ta farko a hedikwatar hukumar, an bar shi ya koma gida inda kuma aka nemi ya sake zuwa ofishin a ranar 10 da 11 ga wata don cigaba da bincike.

Bayan ya je a karo na biyu, ya nemi a ba shi dama ya tafi gida bayan shafe sa’o’i ana masa tambayoyi, lamarin da jami’an hukumar suka ƙi amince wa, inda suka nemi ya gabatar da daraktoci biyu daga wata hukuma ta gwamnatin tarayya da takardun gabatarwa daga ma’aikatansu a matsayin sharuɗɗan belinsa.

Ya bayyana cewa, duk da magiya da lauyoyinsa suka yi waɗanda akwai SAN guda uku a cikinsu, jami’an EFCC’n sun ƙi amince wa sauya sharuɗɗan beli.

A saboda haka ya kwana a hannunsu a tsare kafin sako shi da wayewar gari bayan cika sharuɗɗan belin da suka sanya masa.

Sanatan ya kuma soki hikimar da ta sa aka tsare shi, inda ya yi zargin an siyasantar da al’amarin.

By Babaji