Zaɓen 2027: Pate zai jingine kujerarsa ta ministan kiwon lafiya

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Dukkan alamu sun nuna yiwuwar ministan kiwon lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, zai jingine kujerar sa ta mamba a majalisar zartarwa ta tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda gungun tsofaffin ‘yan-ajinsu da ‘yan-uwa a makarantar garin Bauchi suka neme shi da tsayawa takarar kujerar gwamnan Jihar a zaɓen gama-gari na ƙasa mai gabatowa.

Bisa wannan dalili ne gungun tsofaffin ‘yan-ajinsu na makarantar firamare ta ɗangikka dake Unguwar Bakaro ta garin Bauchi bayan sunyi zaman tattauna wa, suka yanke shawarar shelar goyon bayan su na shi Ministan, na babu wata makawa ya fito gasar yin takarar zaɓen kujerar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓe na shekarar 2027

ɗabbaka bukatar wannan yunƙuri yana ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wa ‘yan jarida wacce sakarataren ƙungiyar tsofaffin ɗaliban, Umar Musa ya rattaba hannu akai a kwanakin baya a garin Bauchi, inda ya ƙara da cewar, nagarta da nasarori da Muhammad Ali Pate ya nuna a shekarun baya, basu misaltuwa ga galiban ‘yan siyasa na Jihar Bauchi da wani zai iya yin tutiya dasu.

Sanarwar tayi jurwaye da kamar haka, “A namu ra’ayin da yaƙini, nasarorin ministan kiwon lafiya da walwalar jama’a na tarayya dake kan karaga a halin yanzu, Farfesa Muhammad Ali Pate ya cimma, da kuma ƙwarewar sa kan wannan fanni, yasa yayi fintinkau wa cancantar duk wani maluƙi dake da’awar ɗalewa bisa wannan kujera to gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen gama-gari na shekarar 2027.

“Mu, a matsayin mu, na waɗanda sukayi makarantar firamare tare dashi, muna alfahari na kasance wa cikin wannan tafiya na ƙoƙarin tabbatar da cewar, Farfesa Ali Pate yayi jagorancin Jihar Bauchi nan gaba kaɗan, kamar yadda muke da yaƙinin zai amshi wannan kira namu na kasance wa ɗan takarar kujerar gwamna a zaɓe Mai gabatowa, haka zalika zamu himmantu dayin aiki tuƙuru, domin ganin damo yakai ga harawa”, a cewar sanarwar.

Don haka, mu, ‘ya’yan wannan ƙungiya tamu ta tsofaffin ‘yan firamare tare da Ali Pate muke tutiya da himmatuwar Pate na wanzuwar cibiyoyin kiwon lafiya, manya da ƙanana, har ma Dana ƙololuwa a ɗaukacin faɗin ƙasar nan, hadi da Jihar Bauchi, domin inganta lafiyar ‘yan-ƙasa.

“A yau, ba gobe ba, wannan tagomashi, ya azamar da ‘yan ƙasa fafutukar samun ingantaccen ilimin, kiwon lafiya, garaɓasa ayyukan gona, muhalli, ingantaccen ruwan sha, tsaro da zaman lafiya, kazalika samun ayyukan inganta tattalin arziki. La’akari da cewar, babu wani mulkin dimokradiyya da zai jiɓanci raguwar majalisar gudanar wa, kamar yadda wasu suke hanƙoron idan batun samun jajiccecciyar majalisar ce, babu halacciyar Jiha da mutum ya kamata ya more rayuwar sa face Bauchi”.

“Bauchi sahihiyar Jiha ce Mai fasalin ingancin rayuwa. Idan ta fannin harƙar siyasa ce, matuƙar Farfesa Muhammad Ali Pate zai amince da wannan kiraye namu, tare da yanke shawarar tsumduma cikin ‘yan takarkarun neman kujerar gwamnan jiha, da igiya ta kwance a gindin kana, ko ace tsallen mutum ta Kai ga faɗuwa kan kujera, husasan ga masu da’awar shugabanci nagari Mai azamar cigaba, kamar yadda gogan namu yake da sarautar ‘Mai Nasarar Bauchi”, kamar yadda Musa ya shelantar.

“Shiga, ko zama ɗan takara wa Pate, ba batune na maganar zaɓe ba, hange ne na bunƙasar Jihar Bauchi, kamar yadda kowa-da-kowa yake alfaharin shaidarwa. Kasancewar sa ya zama ɗan takarar kujerar gwamna, ba batune na son zuciya ko Ida buri ba, Lamarine na bukatar samun ingantaccen shugabanci da yayi daidai da gyauton jama’a, na rashin cuta da cutarwa, haɗi da hangen nesa. Batune na cimma bukatar samun shugabanci nagari da ɗaukacin al’ummar Jihar Bauchi suka daɗe suna nema, wanda kuma yake cike da nagarta, adali mai shimfiɗa sahihiyar hanyar ingantaccen rayuwar bil-adama.

Umar Musa yace, “Tafiya ce dake bukatar jajircewa, ƙwazo da yakana, wacce Farfesa Muhammad Ali Pate zai jagoranta, wacce kuma Jihar Bauchi take da kuzarin zama bisa ƙafafun ta, cikin wadata da haɗin kan jama’a. Muna cike da farin cikin bisa addu’o’in kamar yadda zaɓen shekarar 2

By ukarofi