Hedikwatar Tsaro ta ƙarfafa farautar Turji sa’o’i 24 da kama jagoran ƙungiyar Mahmuda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Alhamis Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta sanar da cewa ta baza komar kama sanannen jagoran ƴan bindigar nan, Bello Turji, bayan da jami’anta suka kama shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Mahmuda, Abubakar Abba.

A ranar Laraba aka kama Abba a yankin Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja bayan samun wani rahoton sirri akansa daga Hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS.

Ƙungiyar, wanda reshe ne na Boko Haram, ta sha kai munanan hare-hare a sassan jihohin Kwara da Neja.

Daraktan yaɗa labaran DHQ, Manjo Janar Markus Kangye a wata hira da manema labarai, ya ce har yanzu suna cigaba da neman Turji ruwa-a-jallo.

Ya faɗi haka ne don bada amsa ga waɗanda suka yaɗa cewa wani malami ya shirya yin sulhu da shi.

Kamar yadda Blueprint ta ruwaito, a kwanaki kaɗan da suka gabata ne babban malamin addini, Sheikh Musa Yusuf da aka fi sani da Asadus-Sunnah yayin wani taron majalisin karatu, ya ce Bello Turji ya sako mutane 32 da aka yi garkuwa da su. Ya kuma ya yi alƙawarin daina kai hare-hare bayan ganawa a lokuta mabanbanta da wasu malamai a maɓoyarsa da ke jihar Zamfara.

Haka kuma ya ce, a yayin haka Turji ya ajiye wasu daga cikin makamansa, lamarin da ya sa ake ganin hakan a matsayin matakin zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Shinkafi ta jihar.

By Babaji