Yadda gyare-gyaren Tinubu ke inganta tattalin arziƙin Nijeriya – Okonjo-Iweala

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa na ingantawa da samar tabbatuwa ga harkokin tattalin arziƙi a Nijeriya inda ta ce gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi suna tafiyar da ƙasar yadda ya dace.

Ta bayyana haka ne a yayin hira da manema labarai jim-kaɗan bayan ganawa da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Ta ce, tattaunawar da suka yi da shi ta ƙunshi ƙaddamar da shirin na musamman don inganta rayukan mata a Nijeriya ta tsarin tattali na dijital, wato ‘digital export economy’.

Ta kuma kirayi gwamnatin tarayyar da ta tanadi tsare-tsaren sauƙaƙa wa talakawa da ke jin raɗaɗin tsare-tsaren tattalin arziƙi na gwamnatin Tinubu.

Duk da ta yaba wa shugaban ƙasar kan tsare-tsarensa na tattalin arziƙi da suka haɗa da cire tallafin man fetur, tsohuwar ministar kuɗin Nijeriyar ta ce dole ne gwamnatin ta tallafa wa ƴan ƙasar.

“muna ganin shugaban ƙasar da gwamnatinsa sun daidaita tattalin arziƙin Najeriya, amma duk da haka sai sun tabbatar da ɗorewar sauyin mai kyau da aka samu zuwa yanzu”, inji ta kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji