SDP a Gombe ta musanta rikicin shugabanci

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) reshen Jihar Gombe ta musanta zargin cewa jam’iyyar ta rabu gida biyu, inda ta bayyana cewa tana nan dunƙule ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Abubakar Buga Daɗawagga, wanda ofishin jam’iyyar na ƙasa ya amince da shi a matsayin sahihin shugaban jiha.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin sakataren jam’iyyar na jiha, Rabaren Jones Nawarke Ngai, ya fitar bayan taron majalisar zartarwar jiha, inda ta nesanta kanta daga wata ƙungiya ƙarƙashin Hajiya Dijatu Baffa, tana kiran hakan shirin siyasa na neman rushe jam’iyyar.

SDP ta yi kira ga mambobinta, jama’a, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da su yi watsi da duk wata ƙungiya da ke ikirarin wakiltar jam’iyyar a jihar banda sahihin shugabanci na Alhaji Sani Abubakar Buga Daɗawagga.

Haka kuma, jam’iyyar ta jaddada biyayyarta ga muƙaddashin shugaban ta na ƙasa, Farfesa Sadik Umar Abubakar, tare da tabbatar da aniyar tsayar da ƙwararrun ‘yan takara a babban zaɓen 2027.

By ukarofi