Ma’aikatar al’adu da yawon shaƙatawa ta Jihar Bauchi za ta inganta gandun dajin Yankari

Spread the love

Daga MU’AZU HARɗAWA a Bauchi 

A ƙoƙarin gwamnatin jihar Bauchi na inganta harkokin yawon shaƙatawa da bunƙasa al’adu don tafiya daidai da zamani, sabon babban Sakataren Ma’aikatar wato Ministry of Culture and Tourism Dr. Chiroma Ahmed Malle ya ziyarci hukumar bunƙasa al’adu da yawon shaƙatawa mai lura da gandun dajin Yankari da Sumu da Lame Burra da tafkin Maladumba don ganin yadda ayyukansu ke gudana.

Dr. Chiroma Ahmed Malle ɗan’iyan Jama’are babban Sakataren ma’aikatar ya ziyarci hukumar ranar Talata 5 ga Agusta, 2025, yadda a cikin jawabinsa ya bayyana jin daɗi game da yadda aiki ke gudana a wannan hukuma. Kuma ya bayyana cewa rashin kayan aiki da gyara a ofishin abu ne da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa zata tashi tsaye wajen ganin gwamnatin jihar Bauchi ta kawo ɗauki ta yadda za a inganta ayyukan hukumar da dukkan gandun dajin Yankari da Sumu da Lame da Maladumba.

Ya ce a matsayinsa na wanda ya yi aiki a wurare da dama zai haɗa kai da daraktocin ma’aikatar don tallafawa hukumar don ta farfaɗo da ayyukanta saboda a samun kuɗin shiga wa gwamnatin jihar Bauchi da tarayya.

Don haka Chiroma Ahmed Malle ya buƙaci ma’aikatan su daure su nuna juriya don yin aikin da zai ciyar da hukumar gaba.

Ya ƙara da cewa ma’aikata na wahala saboda ƙarancin abin sarrafa rayuwa, amma duk da haka a yi haƙuri, suna kyauta zaton Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir zai waiwaisu don inganta yanayin aiki da rayuwar ma’aikata kamar yadda aka ɗauko hanya.

Shi ma shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Bauchi mai lura da gandun dajin Yankari da sauran su, Dr. Mohammed Nasiru Yusuf cikin jawabinsa ya bayyana jin daɗinsa saboda wannan shine farko da daraktocin ma’aikatar da babban sakataren suka ziyarci hukumar don jin yadda aiki ke gudana.

Kuma ya ji daɗi game da nuna damuwa da babban sakataren ya nuna game da rashin kyawun ofis da ƙarancin kayan aiki da suke fuskanta.

Don haka Dr. Nasir Yusuf ya ƙara da cewa matuƙar Gwamna Bala Mohammed ya samu labarin halin da suke ciki ya san zai kawo musu ɗauki ta hanyar yi musu gyara da ba su kujerun aiki da motoci da za su inganta ofishin.

Kuma tuni sun rubuta wa shugaban ma’aikatan jihar Bauchi da kwamishinan ma’aikatar da wuraren da suka dace don ganin an kawo musu tallafin kayan aiki.

Ya ce a yanzu suna da kusan ma’aikata 50, kuma za su yi aiki da su wajen tara kuɗin shiga daga otel-otel da wuraren kallo da na raye-rayen gargajiya da wuraren cin abinci da ke ƙarƙashin kulawar hukumar.

Da haka ne Bauchi za ta yi gogayya da ƙasashen da suke amfana da yawon shaatawa har a samu ci gaba mai ɗorewa.

Dr. Nasir Yusuf ya ƙara da cewa suna da ma’aikata amma akwai masu wasa da aiki don haka za su hukuntasu, kuma ma’aikata da suke aiki tsakani da Allah za su musu abin da ya dace don ganin sun ci gaba don su sauke nauyin da aka ɗora musu.

By ukarofi