Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta gabatar ma gwamnatin tarayya duk wasu tsare-tsaren amsar wutar lantarki mai amfani da iska da ke Lambar Rimi mai ƙarfin Mega 10MW.
Mai baiwa gwamna shawara kan makamashi Dakta Hafiz Ibrahim, ya gana da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya da suka haɗa da babban sakataren ma’aikatar lantarki Mahmoud Mamman, da kuma Darakta Janar na hukumar kula da kayan gwamnati (Infrastructure Concession Regulatory Commission) Mista Jobson Ewalefoh, a cikin shirye-shiryen amsar wurin.
Dakta Hafiz Ahmed, ya gabatar da tsarin da za’a gudanar da wurin akan shi na Special Purpose Vehicle (SPV), da kuma yarjejeniya da kamfanin rarraba lantarki na Kano Electricity Distribution Company (KEDCO).
Darakta janar na ICRC ya yaba ma ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina a bisa shirin amsar wurin, inda yace wurin zai fara amfani da zaran an kammala tsarin gudanar da shi.
Ya kuma ce akwai alamomin nasara a cikin shirin gwamnatin Jihar Katsina wanda, inda ya ce ba wai iya lantarki zai samar wa jihar Katsina ba har ma da ƙarin kuɗin shiga.
Shima Babban Sakataren ma’aikatar lantarki (Ministry of Power) ya ce wannan ƙoƙari na Gwamna Dikko Raɗɗa abun a yaba ne kuma ba ƙaramin nasara bace a siyasar shi, kuma hakan wani cigaba ne a fannin samar da makamashi na zamani a jihar.
An umarci mai baiwa gwamnan shawara da ya gabatar da duk wasu takardun nuna sha’awar amsar wurin ga hukumar ICRC, domin samun cikakken lasisin amsar shi.
Idan aka kammala aikin wannan wuri zai samar da ingantaccen lantarki, samar da ayyukan yi, tare da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
