Gwamnatin Katsina ta raba tallafin kuɗi ga mutane 223 da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin Community Watch, wanda ya wakilci gwamna Raɗɗa a wajen raba tallafin,Malam Yusuf Ibrahim Safana, ya bayyana cewa cikin waɗanda suka amfana akwai mutane 17 daga Malumfashi da 206 daga Sabuwa.

Ya ce dangin waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a harin sun samu N200,000 kowannensu, yayin da waɗanda aka yi garkuwa da su amma daga bisani aka sako suka samu N100,000 kowannensu. Waɗanda suka ji rauni kuwa an basu N50,000 kowannensu.

Malam Safana ya bayyana cewa dangin ‘yan sa-kai da suka rasa rayukansu wajen kare al’umma sun samu N500,000, yayin da mambobin Community Watch Corps da suka rasa rayukansu suka samu N1,000,000 kowannen su.

Ya bayyana wannan tallafi na kuɗi a matsayin wani taimako da gwamna Dikko Raɗɗa ya ɓullo da shi tun hawan sa mulki domin taimaka wa iyalan waɗanda harin yan bindiga ya shafa su rage buƙatar yau da kullum.

Gwamnatin jihar ta kashe fiye da Naira biliyan ɗaya a wajen bada wannan irin tallafi.

Har yanzu ana samun rahotanni kai hare hare na ƴan bindiga a ƙauyen Kudancin jihar inda ake rasa rayuka da sace dabbobi.

By ukarofi