Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban ƙasa Bola Tinubu, kuma saƙanin yadda ake ta raɗe-raɗi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi.
A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa Shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba.
Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya ce Tinubu na nan ƙalau.
“Shugaban ƙasa na nan ƙalau, kuma cikin ƙoshin lafiya yana kuma ci gaba da ganawa da jama’a, kuma ni ma na ji daɗin tattaunawa da shi,” inji Gwamnan.
Baya ga Gwamna Soludon, shi ma takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada da kuma Ministan Kuɗi Wale Edun, su ma sun je fadar don ganawa da Tinubu a ranar ta Litinin.
Gwamnan Soludo dai wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, ya yi kira ga jama’a da su yi gangamin mara wa Tinubu baya, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran bunƙasa dimokuraɗiyya da haƙaka tattalin arzikin Nijeriya.
Kodayake dai ya ki bayyana ainihin abin da suka tattauna ga ’yan jarida, amma dai ya ce ganawar ta su ta yi kyau.
