Hukumar Hisbah a Katsina ta sasanta ma’aurata 6,000

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar Hizbah ta Jihar Katsina ta sasanta ma’aurata 6,000 tare da daƙile ayyukan alfasha a faɗin jihar.
Kwamandan hukumar Dr Abu Ammar ya sanar da haka a hira da ya yi da manema labarai a Katsina.
Da ya ke bayyana irin nasarorin da hukumar ta samu tun bayan kafuwar ta, kwamandan ya ce kafa dokar haramta karuwanci,caca, askin banza da dokar da ta hana masu haya da keke NAPEP da babura ɗaukan mutane da ya wuce ƙa’ida .
“A shekarun baya sana’ar karuwanci ya watsu a jihar amma da kafa dokar haramta sana’ar hukumar ta maida mata fiye da 500 da ke kasuwancin a faɗin jihar wajan iyayen su,” inji Dr Ammar.
Ya bayyana wannan nasara da hukumar ta samu da kuma irin ayyukan ta, al’umma da dama na zuwa wurin su domin buƙatar hukumar ta taimaka ta buɗe reshe a inda suka fito.
Shugaban hukumar ya jawo hankalin al’umma da su kasance masu ba hukumar haɗin kai da goyon baya tare da yaɗa ayyukan su na tsarkake al’ummar jihar.

By ukarofi