Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da wani babban shirin horarwa ga malamai 18,000, tare da fara raba na’urorin koyarwa guda 20,000 domin haɓaka koyarwa da kuma inganta harkokin ilmi a faɗin jihar.
Muƙaddashin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe, wanda ya ƙaddamar da shirin a katsina, ya bayyana shirin a matsayin wani babbar jari da dabaru don makomar yaran jihar.
“Waɗannan ba ƙididdiga ba ce kawai, a’a, jari ce ta dabaru don makomar yaranmu, ta hanyar samar wa malamai kayan aikin zamani da horo mai dacewa, muna daidaita tsarin ilimi da ƙa’idojin duniya don shirya ɗaliban mu su fafata a ƙarni na 21,” in ji Farouk Joɓe.
Ya bayyana tsarin a wani ɓangare ne na cikakken shirin gyara ilimi a jihar, wanda ya haɗa da raba kayan makaranta (uniform) guda 30,000 ga yara marasa galihu da kuma saka na’urorin kyamara (CCTV) a makarantu 130 don inganta tsaro.
Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana wannan shiri a matsayin “wani gagarumin ci gaba” wajen dawo da ingantaccen ilimi a jihar,”kwamishinan ta ce
Ta godewa babban bankin duniya, hukumar ilimin bai ɗaya (UBEC), da sauran abokan haɗin gwiwa saboda goyon bayansu, inda ta yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafawa malamai ta hanyar shirye-shiryen haɓaka ƙwarewa.
Mai gudanar da shirin taimakon cigaban Ƙwarewar Koyarwa na jihar, Hajiya Binta Abdulmumini, ta bayyana cewa, manyan masu horarwa guda 90 za su horar da malamai 18,000. Kowanne malami zai karɓi na’urar koyarwa wadda aka riga aka sa mata shiri-shiryen darasi da kayan koyarwa na zamani.
Shugabar Ƙungiyar Malamai ta jihar, Hajiya Rakiya Shehu, ta yaba da jajircewar gwamnati tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da nasarar shirin.
Har ila yau, jihar ta samar da babura guda 70 ga jami’an sa ido don inganta kula da makarantu, musamman a yankunan karkara, da kuma samar da kayan koyarwa na musamman ga makarantun da ke ɗaukar ɗalibai makafi da kurame.
