Gwamnan Imo ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 104,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar.

Uzodimma ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a daren Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Owerri.

A cewar jaridar Manhaja, kuma kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito, an ƙara mafi ƙarancin albashin daga Naira dubu 76  zuwa Naira dubu 104.

Haka kuma, ya sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi na likitoci daga Naira dubu 215 zuwa Naira dubu 503,  yayin da na malamai a manyan makarantu ya ƙaru daga Naira dubu 119  zuwa Naira 222  da sauransu.

Ya ce ‘yan Jihar Imo sun fuskanci ƙalubale da dama tun bayan hawansa mulki, ciki har da matsalar tsaro, annobar COVID-19, matsin tattalin arziki sakamakon manufofin gyara, da rikici kan mafi ƙarancin albashi da kuma cire tallafin man fetur.

Ya ƙara da cewa idan an biya ma’aikata albashi mai kyau, da a samu nagartar aiki, za a kyautatawa iyalai da saka su cikin farin ciki, kuma tattalin arzikin cikin gida ya na bunƙasa.

Uzodimma ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga na jihar (Internally Generated Revenue) sun ƙaru daga Naira miliyan 400 zuwa sama da Naira biliyan 3 a kowane wata.

By ukarofi