Ba zan fice ba daga Jam’iyyar NNPP, inji Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da jita-jitar shirin ficewa daga jam’iyyar, yana mai cewa ya tsayu wajen ganin ya ƙarfafa ta yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.

Da yake jawabi a taron Majalisar Zartarwar jam’iyyar (NEC) a Abuja ranar Alhamis, Kwankwaso ya ce yana sane da jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai ɗauki mataki mai ƙarfi game da goben siyasarsa, lamarin da a cewarsa ba gaskiya ba ne.

“Bari na yi amfani da wannan damar wajen sanar da ku cewa mu na da jam’iyyarmu, kuma hakan ya mana. Mu na farin ciki. Mun shirya yin komai da ake buƙata don ba sauri mu ke ba”, inji shi.

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa dukkan wata tattaunawa game da zaɓen 2027 za ta zama da murya ɗaya daga jiga-jigan jam’iyyar ne, ba ga iya mutum ɗaya ba.

Ya kuma kirayi magoya bayan jam’iyyar da kada su ruɗu da batun sauya sheƙa da ƴan siyasa ke yi, yana mai cewa da dama daga masu yin haka ba su da alƙibla a siyasa.

Daga cikin ababen da aka cimma a zaman NEC na jam’iyyar akwai kafa kwamitocin riƙo na jihohin Kogi, Gombe, Taraba da Jigawa, da kuma ƙara wa’adin jagorancin shugaban jam’iyyar na Legas.

By Babaji